Kano Pillars: Jihar Kano Ta Yi Makoki Bayan Hadarin Mota Ya Yi Sanadin Mutuwar Yan Wasanni 22
إِنَّا لِلَّٰهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ
Wani mummunan hadarin mota ya yi sanadin mutuwar 'yan wasa 22 daga Jihar Kano wadanda suke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka yi a Jihar Ogun. Hadarin ya faru ne a garin Kura, inda ya bar iyalai, abokai, da kuma al'ummar wasanni cikin bakin ciki.
Abin Da Ya Faru
Wadanda suka rasu sun kasance cikin motar karshe daga cikin ayarin motocin da ke dauke da 'yan wasa daga Jihar Kano wadanda suka fafata a wasanni daban-daban ciki har da Kickboxing da Kokawa. Daga cikin wadanda suka mutu akwai 'yan wasa, masu horarwa, likitoci, da jami'ai wadanda suka sadaukar da rayuwarsu ga ci gaban wasanni.
Bayani Daga Kano Pillars
Alhaji Ali Na Yara Samba, Shugaban Kano Pillars FC, ya fayyace cewa wadanda suka mutu ba 'yan wasan kulob din ba ne sai dai wasu 'yan wasa daga sassa daban-daban na kungiyar wasanni ta Jihar Kano.
Sunayen Wadanda Suka Mutu (Allah Ya jikansu da Rahama)
1. Abdurrahman Muhd
2. Abdul'aziz Auwalu
3. Nasiru Adam
4. Ibrahim Salisu
5. Bashir Bello (Yar Gaya)
6. Imamumalik Umar
7. Bilal Salisu (Jegus Photography)
8. Ashiru Shu'aibu
9. Abdussamad Rabiu
10. Abubakar Isma'il Yakubu
11. Bello Muhd
12. Usaini Garba
13. Isah Usman Aliyu
14. Isah Ibrahim
15. Abdullahi Saleh Trigger
16. Nasiru Abdullahi
17. Aminu Muhammad
18. Shehu Saidu
19. Usman Muhammad
20. Sani Yusuf
21. Muhammad Aminu (Alaja)
22. Hamal Dahiru
Muyi Musu Addua'a
Wannan babban hasara ce ba ga Jihar Kano kadai ba, har ma ga al'ummar wasanni ta Nijeriya baki daya. Mu yi addu'a ga marigayai da kuma iyalansu da suka rage.
اللهُـمِّ اغْفِـرْ لَهُـمْ وَارْحَمْهُـمْ وَعَافِهِـمْ وَاعْفُ عَنْهُـمْ
📌 Allah Ka jikan Su Da Rahama Ya gafarta musu .
Kano Pillars Jaruman Wasanni InnaLillahi Gasar WasanniTa Kasa