Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng
Posts

WASU DAGA CIKIN DALILAN DAKE KAWO YAWAN RUSHEWAR GIDAJE

Dalilan Rushewar Gidaje - Jibia L.G.A

WASU DAGA CIKIN DALILAN DAKE KAWO YAWAN RUSHEWAR GIDAJE (A CASE STUDY OF JIBIA L.G.A)

Da farko, ina ƙara jajantawa ga duk wadanda wannan bala'i ya shafa. Allah Ya jikan marigayi, Ya kuma ba wa mai rauni lafiya, Ya maida mafi alheri.

Bincike na ya nuna wasu dalilan da ke haifar da rushewar gidaje a Jibia (Building Collapse):

1. Jarabawa (Natural Disasters)

Duk wanda ya yi imani da Allah, dole ne ya yarda da kaddara—mai kyau ko mara kyau.

2. Fawundashi (Foundation Problems)

Kamar yadda Hausawa suke cewa, "Tun rangini, tun ran zane." Rashin ingantaccen foundation da kuma gina gini akan ƙasa marar ƙarfi (poor soil) na daga cikin manyan dalilai.

3. Fila da Linta (Column and Beam Design)

Rashin sanya filoli masu ƙarfi a cikin gini, da kuma yin lintel daidai, waɗanda suke ɗaukar nauyin daga rafta zuwa linta, daga linta zuwa fila, daga fila zuwa foundation, daga foundation zuwa ƙasa.

4. Kwaɓi (Mix Ratio)

Wasu mutane suna son zuciya wajen yin mixing—suna Æ™ara yashi fiye da kima, musamman a lokacin haÉ—a siminti da yashi (cement + fine aggregate) ko siminti, yashi, da tsakuwa (cement + coarse aggregate + gravel).

5. Iska Mai Ƙarfi (High Wind Speed)

Iska mai ƙarfi na iya zama sanadin rushewar gidaje, ko da an gina su da ingantacciyar ƙa'ida, musamman gidajen da ke gefen gari ko basu da maƙwabta.

Abubuwan Da Ya Kamata Mu Yi Idan Za Mu Gina Gida:

  • Ka tabbatar ka tuntubi Æ™wararrun masana (Engineers, Architects, DSS) tun daka lokacin da zaka sayi fili har zuwa lokacin gini, ko da a cikin abokanka masu basira.

Allah Ya bamu damina mai albarka.

Khaleed Surajo
ÆŠalibin Civil Engineering
28-05-2025

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment