Changpeng Zhao, or CZ, shi ya gina Binance a July, 2017. Exchange mafi karfi a yau a faɗin duniya ta ɓangaren yawan Jama'a da hada-hadan kasuwanci.
Tabbas CZ ya chanchanci jinjina a wannan duniyar ta cryptocurrency, saboda irin sadauqarwa da yayi har industry ta kai ga wannan matsayin.
🔹 Kafin zuwansa amfani da takardun kudi wajen sayan crypto ba karamin qalubale bane. Amma CZ ya sahhalewa jama'a shiga duniyar crypto ta hanyar p2p, ga uwa-uba ita kanta exchange.
P2P shi ne hanya na farko dana fara samun damar haɗuwa da mutanen kudu da suka jima a harkar Cryptocurrency wanda wasunsu har yanzu ana zumunci.
A wancan lokaci, sanin inda ake sayan Bitcoin sai wane da wane. Su remitano, Paxful, Luno da localbitcoins.
Hmm a wancan lokaci sai dai a bude WhatsApp group ayi ta P2P ko Telegram, a haka ake shiryawa jama'a gadar zaren scams, suyi ta faɗawa.
🔹 Exchanges kafin zuwan Binance suna fashi ido da ido a tsakar rana wajen withdrawal. Wasu coins ɗin sai dai ka hakura ka kyale su a exchange saboda tsadar kuɗin withdrawal.
🔹 CZ shi ya bankaɗo almundahana da babbar kamfanin FTX take kokarin qullawa wanda ciki harda masu faɗa aji a cikin mala'un kasar Amurka.
Wannan jarumta ya dakile projects na scams da dama, sannan shi ya janyowa Mr. CZ tsangwama daga mahukuntan America (SEC).
🔹 Ya tsafta ce industry na Cryptocurrency ta hanyar bijiro da Hackathons da kyankyashe projects da suka zama Unicorns 🦄 a duniyar Crypto.
Daga ciki akwai Matic, Injective, Axie Infinity , Sandbox, StepN, Elrond (MultiversX) da sauransu wanda kowanne jigo ne a nashi ɓangare.
Wannan kaɗan daga abinda Binance suka kafa na inganta industry na Cryptocurrency cikin shekaru bakwai (7) da suka shuɗe.
CZ da SEC 🔥
Watanni biyar (5) baya SEC ta kakaba Binance a kotu tare da ɗaura mata tarar Biliyoyin daloli, sannan daga bisani ta shigar da Shugabanta CZ kara.
A yau wata babbar kotu ta yankewa Mr. CZ hukuncin zama gidan kaso na wata huɗu (4), yayin da DOJ da SEC suke neman a ɗaure CZ na tsawon shekara huɗu (4).
Tabbas munyi kewar CZ a duniyar crypto.
Wace kalma kake da ita akan CZ?