BITCOIN HALVING
Bitcoin mining ⛏️ na nufin hanyar da mutane ke amfani da computer 🖥️ ko mining hardware wajan lissafin complex mathematical problems saboda validating din transaction,idan miner yayi nasarar lissafin complex mathematical problems din daidai zai samu rewards din BITCOIN amatsayin ladan aikinsa shiyasa ake kiran tsarin BTC amatsayin prove of work(PoW),wato kamar ladan wahalar lissafin mai tsauri da yayi nasarar canka dai-dai.
Bitcoin mining ⛏️ Yana da tasiri sosai wajan tsaro(security) da kuma dai-dai ko stability Bitcoin network ta hanyar verifying din transaction,masu mining din BTC suna taimakawa wajan hana almundahana ta hanyar tabbatar da duk transaction din da'akayi valid transaction ne.
Bitcoin halving wani tsari ne da akama BTC saboda rage yawan abinda miners suke samu zuwa rabi(half) bayan network din btc yayi mining din block 210,000,wanda hakan na faruwa kimanin bayan kowacce shekara hudu,bitcoin halving na faruwa ne a yayin da akasamu change a bitcoin mining algorithm.
Bitcoin algorithm na nufin wani tsarin lissafin dake bayyana yanda ake bada ladan(rewards)ko wani block,bayan anyi mining,shiyasa bayan anyi mining din 210,000 algorithm ke rage adadin abinda za'a iya mining zuwa rabi.
Bitcoin halving yana shafar bitcoin network ta hanyar maida bitcoin wahalar mining da kuma daga darajar farashinsa ,kuma hakan na taimakawa wajan control din yawan adadin BTC.
GA MISALIN YADDA HALVING YAKE
A shekarar 2009 ladan(rewards) mining din bitcoin block BTC Hamsin(50) ake samu.
A shekarar 2012 ladan mining block yaragu da rabi zuwa ashirin da biyar(25).
A shekarar 2016 ladan mining yakara raguwa da rabi zuwa shabiyu da rabi 12.5 BTC.
A shekarar 2020 ladan mining block yakara raguwa zuwa 6.25 BTC.
Ana sarai 2024 da zamushiga za'ayi halving wanda muke sarai mining block zai koma 3.125 BTC, haka mining block zai cigaba da raguwa har zuwa lokacin daza a gama mining din adadin BTC milliyan ashirin da daya(21 million),wanda haka zai faru a shekarar 2140 idan muna da tsawon rai.
Abin lura bawai halving yana nufin BTC zai yi tashin da bai tabayi ba,amma yana cikin dalilan dake nuna BTC zai iya tashi Shin idan aka gama mining din BTC mai zai faru
Insha Allah zanxo da cikakkiyar bayani a rubutu na gaba
Tajuddeen Y Hassan accept challenge .