YAU ZAMUYI FASHIN BAƘI AKAN RUG PULL PART TWO
* Menene Rug Pull?
* A ina akafi yawan yin Rug Pull?
* Yaddan zaka kare kanka daga faÉ—awa Rug Pull.
* MENENE RUG PULL?
Rug Pull wata zambace da ake yinta a Masana'Antar cryptocurrency inda masu Token suke watsar da Project su gudu da kuÉ—in mutane.
Rug Pull yana faruwa ne yawanci a Decentralized Finance (DeFi) ecosystem, musamman a Decentralized Exchanges (DEXs), ta yaddan 'yan damfaran suke ƙirƙirar Token su sashi akan Decentralized Exchanges (DEX), sannan su haɗa shi da manyan cryptocurrency kamar Ethereum a matsayin Pair.
Da zarar wasu adadi mai yawa na mutane sun canza ETH ɗinsu da Token ɗin, wato sunyi Swapping da ETH, sai masu Token ɗin su janye Liquidity Pool, sai darajar Token ɗin ya dawo Sifili, wato Zero. Wasu lokutanma masu Token ɗin sukan ƙirƙiri wani zance da zaisa wa mutane tsammani susa a Social Media ɗinsu, kamar Telegram, Tweeter da Facebook bayan sun maida wani adadin kuɗi mai yawa a Liquidity Pool ɗin Token ɗin don sawa mutane tsammani.
* A INA AKAFI YAWAN YIN RUG PULL?
Ana yin Rug Pull ne yawanci akan Decentralized Exchanges (DEXs) saboda waɗannan nau'ikan Exchanges ɗin suna bada damar ɗaura Token kyauta kuma ba tare da tantancewa ba, ba kamar a Centralized Cryptocurrency Exchanges ba. Bugu da kari, ƙirƙirar Token akan Blockchain Protocol na buɗe (Open Source) kamar Ethereum yana da sauƙi kuma kyauta ne, masu damfara suna amfani da waɗannan abubuwa biyu ne don cimma burinsu.
* YADDA ZAKA KARE KANKA DAGA FADAWA RUG PULL
Yi la'akari da cewa Decentralized Exchanges kamar Uniswap algorithmically suna ƙayyade farashin Token a Liquidity Pool dangane da adadin kuɗin da yake ƙasa. Don tabbatar da cewa ba ka faɗa a Rug Pull ba, duba yawan Liquidity Pool ɗin Token wannan shine mataki na farko. Dole ne ka bincika idan akwai makulli akan Pool ɗin Token ɗin. Yawancin Project masu nagarta sukan kulle Liquidity na tsawo lokaci.
Wata babbar hanyar yiwuwar Rug Pull ita ce tashin Token cikin sa'o'i. Misali, from 0 to 50× cikin sa'o'i 24. Wannan dabarar zaisa wanda bai sayi Token É—inba ya saya don gudun kar ayi babushi (FOMO).
Insha Allah a gaba zamuyi bayani akan yadda zaka gane idan an rufe Liquidity É—in Token, kuma harna tsawon wani lokaci?.
Allah ya kare mu da dukiyarmu daga mazambata....