Dyor : Ma'anar Kalamar Dyor A Yaren crypto currency Da kuma Forex.

APK Store
0

 


Fashin Baki  Akan Kalmomin 4 Da Nake Yawan Maimaitawa Tun Dana Fara Crypto.

 DYOR

A crypto space idan akace DYOR ana nufin do your own research before investing! Wato kafin ka saka dukiyarka Ka sayi Wani crypto currency Yana da kyau kayi iya binciken ka Domin sanin dalilin da zaisa ka saka kudinka aciki! DYOR ya hada dukkan Wani Abu da ake buqata kamar!

Team behind the project, dole ka bincika background na team' shin wanne skill suke dashi a fannin TECH tare da tracking record nasu' shin sun taba aiki a Wani project Kuma wanne mataki wannan project yataka , may be zaka iya ganin hotonsu acikin White paper nasu abinda zakayi sai kayi Saving na hoton kaje cikin chrome kayi amfani da google lens akan hoton Wanda zai baka fuskoki irin na wannan hoton saika duba Koda fuskar anan zaka iya ganin dukkan Wani Abu da ya shafi Mai wannan hoto! So hakan zai baka damar tabbar da abinda suka fada na skill ko suna dashi ko Basu dashi! 

Dukkan Wani project suna da White paper Wanda anan suke bayanin irin yanda zasu tafiyar da project nasu da use cases da wannan project yake dashi misali Wata matsala zaiyi solvin) idan karanta White paper bazai gamsar da kaiba direct saika tafi coingecko kayi searching na wannan coin anan zaka samu Abubuwa kamar

 total supply,

 max supply ,

 Circulation supply, tare da tokenomincs yanda akayi distribution da economy model, sai Kuma ka duba audit Wanda ya qunshi Abubuwa kamar yanda aka amince da smart contract ta hanyar security and Law compliance da anty money laundering! 

Bayan Nan sai kayi copy na contract address katafi scanner' binance scan ko etherscan ya danganta da chain da coin din yake akai sai kaje kayi paste anan zaka samu Abubuwa kamar haka zaka iya ganin yanda ake transaction akan coin din da Kuma yanda manyan whale da exchangers suka debeshi! 

Bayan Nan saika tafi social handle domin ganin adadin users engagement da Kuma sentiment daga users tare da bincikar yanda wannan project yayi partnership da collabration da manyan kamfanoni da Kuma sauran organization Wanda hakan shine yake yanke hukuncin goben project! 

Project network abinda ya shafi transactions volume transaction fees , scalability da Kuma ability na yanda network yake handling large transaction shima zai baka damar sanin hakikanin coin domin a yanzu miners suna duba yanayi na qarfin da saurin network na project kafin suyi interaction dashi.


#DYOR

#is_a_risk

#not_financial_advise

#invest_what_you_can_afford_to_lose


Fashin Baki  Akan Kalmomin 4 Da Nake Yawan Maimaitawa Tun Dana Fara Crypto.


DYOR; Ma'ana kayi binkice naka na karan kanka, kada ka taba daukar magana ta a matsayin hujja. Duk abinda nake fada ina fadinsa ne a karan kaina, da kuma abinda na fahimta a iyakar tunani da ilimi na. Maybe idan kaje binkice ka nemo abinda yafi nawa, saboda haka idan ka nema sai ka rike hujjar ka.


IT'S A RISK; Idan ma ka yarda da abinda na fada, ko kuma kaje kayi binkice naka ka gamsu akan abinda daka binkito. Toh ka sani; Abinda zaka shiga nan fa kasada ne, babu tabbaci akan sa. Ta yiwu aci riba, ta kuma yiwu a fadi koma ya ruguje. Wannan ko a gurin taruka ina yawan fada.

NOT A FINANCIAL ADVICE; Duk abinda kaga na rubuta, ko na fada. Ba shawara nake baka ka saka kudinka ba, wannan shine abinda nake yawan fadawa duk wanda ya kirani yace na basa shawara akan wani abu. Ko kuma na rubuta a social media nakan yawan Maimaitawa. Saboda nasan dabi'ar mutane.

INVEST WHAT YOU CAN AFFORD TO LOSE; Idan ma kaji ka yarda kuma ka gamsu cewa zaka saka kudinka akan wani abu da kaga ina yi, toh ka tabbatar ka saka kudin da kafi karfin su. Nima haka nake yi, duk asara bata da dadi. Amma idan kayi asarar dukiyar da ka tabbatar kafi karfin ta. Toh asarar zata zo maka da sauki.


Allah Yasa Mu Dace!

Post by msz......

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.
Post a Comment (0)
Our website uses cookies to enhance your experience. Learn More
Accept !