Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

Menene :'Layer one', 'Layer Two' da kuma 'Layer zero' A Cryptocurrency ?


Part Two 

Daka ta! Ka karanta, ka fahimci wani abu game da 'Layer one', 'Layer Two' da kuma 'Layer zero'. 

Bitcoin da Ethereum sune projects mafiya girma a tarihin kasuwar Crypto, haka zalika kowanne da akwai dalilai da suka sa akayisa saboda a magance wata matsala data damu mutane.


Bitcoin:

Babbar matsalar da BTC yake magancewa itace ta matsalar a samar wa da mutane hanyar da zasu ajiye dukiyar su, ko su tura ta ga wani, ko wani waje ba tare da an samu wani É—an tsakiya ba (kamar bankuna ko gomnati). Ana samun matsalar wahalhalu, iyakance maka abinda kake da iko dashi na dukiyarka, jinkiri, chaji, ko haraji daga bankunan gargajiya da gomnati.


Ethereum: Ethereum tazo a bayan BTC, a irin zubin tsarin da Ethereum take dashi, ana iya amfani da ita wajen yin duk irin waɗancan abubuwan da BTC yake yi, sai dai ba don haka kaɗai akayi Ethereum ba, ba iya manufar da Ethereum suke so su cimma ba, Ethereum an ƙirƙireta ne musamman don a sauƙaƙa wajen amfani ayi amfani da 'Smart contracts' a ƙirƙiri 'Decentralised Application' akan Blockchain ɗin Ethereum.


A takaice dai, Bitcoin shine farkon abinda akayi akan Blockchain, amma ba'a yi shi don a É—aura wasu 'Applications' É—in akan ba, shi kawai ya kawo sauÆ™in transactions ne, yayin da Ethereum kuma tanayin duk abinda Bitcoin takeyi, amma ita ana iya É—aura abubuwa da yawa akan Blockchain É—inta. Shiyasa ake samun Coins da yawa dq ake É—aurawa akan ERC20, amma ka taÉ“a jin wani Coin akan Bitcoin Blockchain? (Bazamuyi maganar BRC20 ba anan don kar a rikita jama'a). 


Bayan zuwan ETH ne fa da wannan technology É—in aka fara zuwa da Blockchains kala-daban-daban irin su XRP, BNB, Cardano, da sauran su har zuwa yau É—in nan kowanne da matsalar da yazo yake maganin ta. WaÉ—annan Blockchains É—in sune ake kira da LAYER ONE. 1️⃣


LAYER TWO:

Akwai wasu abubuwa guda uku da ake siffanta Blockchain dashi, sune: Decentralization, Security, da kuma Scalability.


Kusan a duk wani Blockchain da muka sani, sai dai ya É—auki biyu daga waccen siffofin su bar É—aya, bazaiyiwu Blockchain yazo ya iya cimma waccen abu guda ukun ba (Please mu ajiye maganar CoreDao anan kar mu rikira jama'a). Ethereum da mukayi magana a sama sai ta É—auki Decentralization da Security sai ta bar Scalability. 'Scalability' yana nufin rashin saurin Transactions.


Don a magance wannan matsalar ta rashin saurin Transactions akan Ethereum, tunda tana da Security, da Decentralization, kuma ana iya É—aura wani abu akan ta, sai aka zo da fasahar Layer Two. Fasahar a É—aura wani Blockchain É—in akan Ethereum, don ya magance matsalar rashin sauri (Scalability).


Misalin Layer Two Blockchain sune: Optimism, Arbitrum, Zksync, da Polygon ZkEVM, dukkan ninsu wasu Blockchains É—inne da aka É—aura su akan Ethereum don su magance waccen matsalar da ake fama da ita.


Layer Zero:

A wannan zamanin muna cikin Lokacin da muke da yawaitar Blockchains da yawa (Layer one Blockchains da Layer Two Blockchain), sai dai akwai wani Æ™alubale da ake fama dashi na rashin wata hanya guda É—aya da Blockchains É—innan zasuyi mu'amala da juna, misali kana da wasu kuÉ—i acikin wani Coin akan Blockchain É—in Ethereum, sai kake son siyan wani Coin É—in akan Blockchain É—in POLYGON, Layer Zero sunzo ne don su samar da hanyoyin da mutane zasuyi mu'amala da Blockchains baki É—ayansu cikin sauÆ™i. 


Wannan a taƙaice kenan!

Ubangiji Allah ya taimake mu ya bamu sa'a.


Anyone who knows these words can access your funds. Before importing to other wallet make sure it supports doginals protocol.

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment