Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

ME AKE NUFI DA PROOF OF WORK A BLOCKCHAIN TECHNOLOGY.

 

 


A SAUKAKE.


PROOF OF WORK: Malamin lissafinku ya baku jarabawa mai wahala, sai kai kuma kaci jarabawar ta hanyar bada amsa daidai, sakamakon haka malamin ya baka kyautar yaba kokarinka.


A BLOCKCHAIN.


Miners kamar malami ne, sai NECO suka bashi gyara jarabawar dalibai, kowacce jarabawa sai ya dauko ta ya karanta sannan ya bada Mark gwargwadon yadda aka amsa jarabawa. Idan an tashi sallamarsa za'a sallame shine gwargwadon yawan takardun da ya kammala MARKING.


Duk Transaction din da ake yi a cryptocurrency bayanin su yana tattare ne a cikin block (kamar wani littafine da ake rubuta bayanan mu'amalolin da suka wakana) Su kuma Miners suna bin kowanne Block su tabbatar tare da tantance Mu'amalolin da aka yi. Duk block din da Miners suka gama tantancewa za'a aje shi a gefe a bude wani Block din sabo.


YADDA ZAKA GANE.


Kaine kana da shago, duk abinda ka saya da duk abinda aka saya kana rubutawa a littafi. Lokacin da littafin ya cika zaka bude sabon littafi, sai ka kira wani masani lissafi ka bashi littafin ya hada maka lissafin guri daya. Ma'ana maimakon ka copy gaba daya abinda ka rubuta sai ya lissafa total din abinda ka saya da abinda ka sayar. Kai kuma sai ka rubuta TOTAL din a sabon littafin da zaka fara recording wanda hakan zai baka damar hada lissafin gaba daya littattafan a guri daya.


To kamar haka Miners suke aiki a blockchain. Duk wani transaction da aka yi ana aje recording dinsa ne a cikin blockchain, idan block ya cika kafin a bude sabon block Miners suna hada lissafin tsohon block din domin a saka a sabon block din da za'a bude wanda ta haka ne lissafi zai tafi daidai batare da an samu giɓin lissafi ba. To gwargwadon aikin da Miner yayi gwargwadon ladar coin din da za'a bashi.


A bankunan gargajiya da muke dasu ma'aikatan banki sune ke tantancewa tare da tabbatar da duk wata mu'amalar kudi da aka yi a bankin. A blockchain kuma Miner ne ke aikin tabbatarwa tare tantancewa kowacce mu'amala.


PROOF OF WORK fahimtar yadda yake simple ne. Ba lallai sai a blockchain ake amfani da wannan ba. Ko aiki ka ba lebura bayan ya gama kace ya nuna maka aiki, bayan ya nuna maka ka sallame shi. Aikin nan nashi da ya nuna maka shine ya tabbatar maka da yayi aikin, wannan tabbatarwa ita ce "Proof of Work"


In memories of Nasir I. Mahuta.

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

Post a Comment