SHIN KASAN ME AKE NUFI DA DEXS TRADING.

APK Store
0

                               DARASI GAMEDA DEXS TRADING

Sanin kan mu ne akasarin Coins ɗin da muke Trading dasu a DEXs Sabbin Ƙyanƙyasa ne da yawan su ko Price basu fara nunawa a Wallet ɗin mu ba,kawai muna amfani da DEXs Tools ne wurin ganin Price da kuma Adadin MARKETCAP ɗin su,Wannan dalilin yana daga cikin dalilan da suka sanya Token ɗin basa Respecting na Candlestick Patterns Dan haka babu buƙatar koda yaushe sai mun duba Candlestick Patterns yayin Trading a DEXs

A yadda kasuwar Cryptocurrency take a yanzu Manipulation yayi yawa,wajibi ne ka nemi wasu Strategies na shiga Kasuwar domin yin Trading Musamman DEXs Trading yafi Risk akan CEXs Trading a fahimtar mafi yawan Traders.

bayan na duba Token sosai naga Ingancin sa musamman Liquidity Locked,Burned,Buy tax and Sell tax,Sellebale or Honeypot,Holders and Investors,Community and Shilling,a ƙarshe na kan Duba Source Code domin tabbatar da Security na token,duka waɗannan research na kan yi su Under 20 Minute ne,Sai kuma nayi amfani da...

Strategies na "SCALPING TRADING" da zarar na shiga na fita da Profit ɗina idan token ɗin yayi ƙasa na duba yiwuwar sake shigar sa Saina sake shiga idan yayi Sama na kuma Fita,amma Wannan Strategy ɗin fa a Sabon Token akeyin sa bai fiya yiwuwa a Tsohon Tokens masu Manyan MARKETCAP ba kamar $1M to $10 MarketCap.

Wannan token ɗin dake jikin Hoton ƙasa a 13k MarketCap na shige shi cikin Minti 20 yaje 36k har yanzu danake rubutun nan Saida na duba shi yana 40k,kuma Abune mai Wahala ya sake komawa 13k a ƙaramin Lokaci duba da yadda yake Sabon Ƙyanƙyasa ne hankalin manyan Investors baije kan shi ba har yanzu,kuma ko ba komai na samu 1x na fita Alhamdulillah!.

Note:

Wani Dan tsokaci nakeso nayi gameda dex maganar gaskiya ana samun kudi acikin dex domin dikkan wani trader yayi amannar cewa dik token dinda kagani a cex tofa da dex yafara kuma sai yabada kudi masu yawa kafin kaganshi a cex 

To amma sai dai wani hanzari ba guduba majority tokens dinda ake kirkira a dex yanzu scam ne zan iya cewa 80% na tokens dinda ake kirkira yanzu scam ne daga cikin 80% dinnan masu dama damar sune wa yanda za afara trading dinsu daga baya su damfari mutane irin wa yannan tokens din basa wuce kwana 2 zuwa biyar wasuma aranar za aci kasuwar a watse sannan irin wa yannan tokens zakaga dik iya bincikenka daga karshe matukar bakayi taka tsantsanba sai an ruftaka daga cikin 80% dinnan dai akwai wa yanda kana fara bincikenka zasu nuna maka matsiyatanne zakaga akwai honeypot aciki ko transferable paused ko mintable daidai sauransu yayinda wancan kashi na farko din zakaga yacika wannan ka idojin 

 Yana daga cikin abinda ze kara fitomaka da irin wa yannan tokens din afili shine zaka kwata kwata basu bayyana Kansu ba imma a social media ko a website atakaicedai bakada inda zakaga hakikanin masu tokes dinnan to kaga tin anan zakafara yiwa kanka tambayoyi taya za ayi mutum yakasa haja kuma yaki bayyana kansa kamar yadda akasan sauran tokens da coin shin boye wane mutum anya yana nuna alamar gaskiya a lamarinnan kuwa .

Yakai Dan uwa katsaya ka nutsu idan zakayi investing a dex domin ba kamar cex bace yau idan aka gudu da kudinka ba Wanda zaka kaiwa kuka 

Domin kaji sunan wajenma kamar haka decentralized exchange 


Yauwa sai magana akan sauran 20% din inda nace 80% scam ne  to kaga dole na lalubo cikon 20% din inda munsan lissafin 100% ne sai nace 80% 


Muje zuwa sauran 20% 


Daga cikin 20% din sumafa akwai scammers amma susukafi karanci daga cikinsu akwai wanda project dinsu yake kaiwa gagaci akwai kuma Wanda shot term project ne kardai rubutun yayi tsayi wannan rubutu nawa ba financial advice bane sannan na Dan tsakuro

it's not Financial Advise  DYOR.

Post by Maaroop Mustapha Muhammad

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.
Post a Comment (0)
Our website uses cookies to enhance your experience. Learn More
Accept !