CEO na NNPC, Engr. Bashir Bayo Ojulari, Ya Kira da Akwataccen Sauyin Makamashi a Afirka.

APK Store
0


CEO na NNPC, Engr. Bashir Bayo Ojulari, Ya Kira da Akwataccen Sauyin Makamashi a Afirka.

A jiya a birnin Lagos, Engr. Bashir Bayo Ojulari, Shugaban Kamfanin NNPC Ltd., ya gabatar da jawabinsa na buÉ—e taron SPE Nigeria Annual International Conference and Exhibition (NAICE 2025) mai taken: Building A Sustainable Energy Future: Leveraging Technology, Supply Chain, Human Resources, and Policy.

Ojulari ya jaddada bukatar yin sauyin makamashi cikin daidaito a nahiyar Afirka, yana mai cewa: Sauyin makamashi bai kamata a tilasta shi ba, sai dai a tattauna shi, a daidaita shi da yanayinmu, sannan a kimanta shi.

Ya bukaci Afirka da ta tsaya da kafarta a fagen makamashi ta hanyar kyakkyawan shugabanci, bin yarjejeniya, da gaskiya. Ya kuma nemi a mayar da iskar gas na halitta a matsayin matakin wucewa daga makamashin carbon, da amfani da kudaden mai wajen habaka makamashin sabuntawa, ilimi da ababen more rayuwa.


Ojulari ya roƙi hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki domin jawo jari, bunkasa fasaha, da kuma karfafa matasa ta fannin STEM da ƙwarewar green skills, yana mai cewa: Ya zama dole mu ba matasanmu damar ganin fannin makamashi a matsayin dandalin ƙirƙira, haɗin kai, da cancantar duniya.

Tags

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.
Post a Comment (0)
Our website uses cookies to enhance your experience. Learn More
Accept !