Shafukan da Zasu Amfane Ku
Shafi | Bayani | Adireshin Yanar Gizo |
---|---|---|
TVET | Shafin koyar da fasahohi da horo na sana’o’i daban-daban. | www.tvet.education.gov.ng |
YEIDEP | Shirin tallafawa matasa da horaswa da samar da ayyuka. | yeidep.org/register.php |
LEEP | Shirin Labour Employment and Empowerment Programme na samar da ayyuka da horo. | jobs.leep.gov.ng |
NATEP | Shirin National Automotive Technicians Development Programme don horar da masu sana’ar gyaran motoci. | natep.gov.ng |
GIGS | Shafin tallafawa matasa da ayyukan yi na gaggawa. | gigs.niya.gov.ng |
Karin Bayani Kan LEEP:
LEEP na ba da damar samun ayyuka da horo ta hanyar dandamali na zamani. Yana hada kai da hukumomi da kamfanoni don samar da dama ga matasa. Za ka iya yin rajista, neman aiki, da samun horo kyauta a shafukan LEEP.
Yadda Za Ku Fara:
1. Ziyarci ɗaya daga cikin shafukan da ke sama.
2. Yi REGISTER (rajista) ta hanyar cike bayanan da ake bukata.
3. Zaɓi jiha da mazaba ko fanni da kake sha’awa.
4. Bincika ayyuka ko horo da ake bayarwa.
5. Aika koke ko tambayoyi ta imel ko lambar waya da aka bayar a shafukan.
Wadannan shafukan na daga cikin manyan hanyoyin da gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu ke amfani da su wajen tallafawa matasa da samar da ayyukan yi a Najeriya. Ku yi amfani da su domin inganta rayuwarku da samun damar aiki.