GUJI WANNAN KUSKURE UKU MASU TSADA IDAN KANA SHIRIN SAYEN LAPTOP
Kafin ka kashe kuÉ—inka wajen siyan sabon laptop, É—an dakata ka karanta wannan rubutu.
Zai iya ceton ka daga damuwa da ɓarnar kuɗi.
Ga wasu manyan kuskuren da mutane ke yawan yi idan suna sayen laptop:
1. Siyan Laptop Mai Ƙarfin Gaske Don Aikin Ƙarami
Idan dai amfani da kake yi shine karatu, lilo a intanet, ko kallon fina-finai kawai — ba sai ka siya Core i7 da 16GB RAM ba.
Amma idan kana aikin design, video editing, ko wani nauyi — kada ka siya Core i3 da 4GB RAM.
Ka siya bisa ga bukatarka, ba wai kawai don suna ko kyan suna ba.
2. Rashin Tambayar Garanti
Wasu sukan biya kuÉ—i su tafi, ba tare da sun tambaya ba:
"Me zai faru idan abu ya lalace bayan na siya?"
Koda garanti na kwanaki 7 ne — tambaya.
Hakan na nuna cewa mai sayarwa yana da tabbaci akan kayansa, kuma kai ma zaka samu kwanciyar hankali.
Ni dai nawa garantin wata guda ne.
3. Watsi da Zabin Sabuntawa (Upgrade)
Wasu laptop ba za a iya Æ™ara musu RAM ko SSD ba — komai ya daure.
Idan ya fara jan aiki, ka makale da shi.
Ka tambaya idan za a iya ƙara memory ko storage nan gaba.
Wannan yana tsawaita rayuwar laptop É—inka.
Shawarata ta ƙarshe:
Kada ka gaggauta. Kada ka bari kyau ko arahar kaya ya ruÉ—e ka.
Ka tambayi tambayoyinka. Ka duba gaba. Idan ba ka san wanda ya dace ka saya ba, sai ka tuntube ni — zan taimaka da fara'a.
Ina nan a gare ka.
Ka sa kuÉ—inka yayi maka aiki, ba wahala ba.
0 Comments