Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

Karin Magana: 120 Hausa Proverbs & Their Deep Meanings (Full List)

Karin Maganganu da Ma'anoni - Hausa Proverbs

Hikimomi da Karin Maganganu tare da Ma'anoninsu a harshen Hausa

Maraba da zuwa wannan shafin namu mai albarka

Gabatarwa

Daga tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al'ummar Hausawa.

Karin Maganganu - Kashi Na Daya

1. Abin rabone, aure mace da ciki.
(Ana amfani da wannan karin magana ne a lokacin da aka samu wani abu da ba'a taba isammanin samu ba).
2. Daga Um sai Um, wai uwar gulma tayi cikin shege.
(Ana amfani da wannan karin magana a yayin da wani abin kunya ya faru da wani mai yawan kawo gulmar wasu).
3. Ina ruwan wani da wani, wai mahaukaci yayi bako.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da aka kawowa mutum zancen abinda bai shafeshi ba).
4. Allah mai halitta, wai jaba ta kalli bakin mijinta.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da aka ga wani da wata irin halitta mai ban mamaki.)
5. Tsugunne bata kareba, an sayar da tsohuwar mota ana auro tsohuwar karuwa.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da ake isammanin an kummala wani abu sai kawai wani abun yarfado makamancin wanda aka kummala.)
6. Za'a kuma, wai anci tuwon sadaka an hana maye.
(Ana amfani da wannan karin magana yayin da mutum yaji wani abu a da ya kamata yaji, sai yaji a inda ba anan ya kamata yaji ba.)
7. Da abin ne, wai an raba nika da akuya.
(Ana amfani da wannan karin magana idan mutum ya nuna yama dashi.)
8. ganin araha, zubawa Ungulu kwan zabi.
(Ana amfani da wannan karin magana yayin da aka samu abu har ya yi yawa ana lalatashi.)
9. Abin ban haushi, toshi da rogo.
(Ana amfani da wannan karin magana lokacin da mutum ya ga abinda ya bashi haushi.)
10. Wa ya isa ya fada, wandon sarki ya yage.
(Ana amfani da wannan karin magana akan wala magana da mutum ba zai iya furtashi ba.)
11. Kaima dai ka fada, wai an yiwa 'ya'ya mugun mili.
(Ana fadin wannan karin magana a yayin da aka aikata wani abu da bai dace ba, kuma wani ya fadi rashin dacewar yin hakan.)
12. Ai sai kayi tayi, wai kârûlvi taji me wa'azî.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da ake fadawa mutum wani abu da bai yarda dashiba.)
13. Zancen kake so, ance da gwauro ya iyali.
(Ana amfani da wannan karin magana yayin da aka zo da wata magana don tsokana.)
14. Samun wuri, hana kishiya tarî ranar sallah.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da aka ga mutum ya aikata abu a wajen da bai kamata sa ya aikata ba.)
15. Alkin banza, harara a duhu.
(Ana amfani da wannan karin magana idan mutum ya aikata wani abu na sakarci.)
16. Ba shiga ba fita, wai an ba mahaukaci gadin kofa.
(Ana amfani da wannan karin magana idan aka sanya dokar hana wani abu.)
17. Ba da ni ba, gada a makabarta.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da ake neman mutum ya yi wani abu, sai ya ga ba zai iya yin ba.)
18. Gane mini hanya, wai makaho ya so guima.
(Ana amfani da wannan karin magana a yayin da ake magana akan wani da aka aikata da bai kamata ba.)
19. Allah yayi, aure da mara kwabo.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da wani abu ya faru wanda ba a yi tsammanin faruwarsa ba.)
20. Ba a kin ta mutane, wai ance da barawoya gudu.
(Ana amfani da wannan karin magana yayin da aka ba mutum wata shawara kuma ya yarda da ita.)
21. Matsayi kenan, wai karuwa a amalanke.
(Ana amfani da wannan karin magana yayin da mutum ya ga wani abu da ya burge shi.)
22. Bari inyi takaina, gwarro ya kona gidansa.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da mutum ya aikata wani abu a waje, kuma yana nufin barin wajen.)
23. Dadi kan dadi kenan, kunama ta harbi gyambo.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da wani abin farin ciki ya samu sau biyu a lokaci guda.)
24. Kayyasal!!, mai gwalando ya ci karo da turmi.
(Ana amfani da wannan karin magana ne yayin da aka fadi wani abu da ya baiwa mutum mamaki da tausayi a lokaci guda.)
25. Kanku akwai, wai mahaukaci ya fada rijiya.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da aka zo wa mutum wani al'amari da bai shafe shi ba.)
26. To ai haka ya fi, wai an sayar da gonar rago an siya masa fura.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da aka fadawa mutum wata magana da ya gamsu da ita.)
27. Kun raba min hankali, ance da rago sha fura ka koma aiki.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da aka umarci mutum ya aikata abu biyu a lokaci guda.)
28. Yau na ga ta kaina, wai barawo a hannun mata.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da mutum ya ga wani abu da ya fi karfinsa.)
29. Ai duk cikin aikine, dan kodago ya kayar da mai gona.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da mutum ya aikata wani abu da ake ganin ba haka bane, shi kuma yana ganin haka ne.)
30. Wadata, shuka da bakin buhu.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da aka ga ana lalata wasu kayan amfani.)
31. Gariin dadi na nesa, wai ungulu ta leka masai (shadda)
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da mutum yaga wani abu daya kamata ya mallaka amma bashi da halin mallaka.)
32. Me zan gani, wai namiji da suna hajara
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da mutum yaga wani abin mamaki)
33. Abu bai yi dadiba, wai anyi da mutum yaji
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da wani al'amari ya faru da ba'a so ya faruba)
34. Zamani ya tarar damu, wai mura ta kama kwado.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da aka ga faruwar wani bakon abu da ba'a san dashiba)
35. duniya juyi-juyi, kwado ya fada ruwan zafi.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da mutum ya isici kansa a wani yanayi da bai sababa)
36. Wata sabuwa, ance da bagwari yace tabbatyada.
(ana amfani da wannan karim maganane a lokacin da aka zowa da mutum wani abu da yake ganin zai bashi wahala)
37. Kai dai kaga mutum, ance da bamaguje samu malam.
(ana amfani da wannan karim maganane a lokacin da wani yayi wani abu da ba'yi zatoba)
38. Ina sam, wai an hada soja da Allah.
(ana amfani wannan karim maganane a lokacin da mutum ya ga wani abu bazai yuwuba.)
39. Mai gaba daya kenan, haihuwar jariri da hakora.
(ana amfani da wannan karim maganane a lokacin da akayi abu da yawa a lokaci daya)
40. An kuma, karuwa ta haifi dan daudu.
(ana amfani da wannan karim maganane a lokacin da aka maimaita wani abu daya faru)
41. Me yañ raina, cin tsiren mata.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da mutum ya samu abin da yake so, ake tsokanarsa.)
42. Zancen banza kenan, zakara ya taka wuka.
(Ana amfani da wannan karin magana ne a lokacin da mutum ya ji wata magana mara ma'ana.)
43. Ka ji dai dashi, wai ciwon ajali a dan yatsa.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da mutum ya zo da wata shawara da ake ganin ba mafita akanta.)
44. Iya yi, cin dambu da tsinke.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da mutum ya ƙyale aikata wani bakon abu.)
45. Sabon salo, zaman makoki da garaya.
(Ana amfani da wannan karin magana ne yayin da mutum ya zo da wani sabon salo na wani abu.)
46. Batan basira, rokon Allah da goge.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da mutum yayi wani abu mara ma'ana.)
47. Gwalangwalaso, zuwa kashin rana da fifila.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da mutum yazo da sabon abun da ba'a san dashiba)
48. Abin da kamar vurya, wai gurguwa da aure nesa.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da akasinar da mutum wani abu da yake ganin zai bayar da wahala)
49. Son a sani, tusa a lasfika.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da mutum ya aikata wani abu don mutane su sani)
50. Tsaftar Biri, kashi a moda
(ana amfani da wannan kalmar ne a lokacin da mutum yayi tsafta ya kumayi kazanta lokaci daya)
51. Duk daya, makafi sunyi dare.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da mutum ya samu abin da bai yi zaton samu ba.)
52. Ya fi dai babu, an haifawa bafillatani bakin jariri.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da mutum ya samu abin da bai gamsar da shi ba.)
53. Ba muhallinta bane, an sawa kuturu angwa ta zame.
(Ana amfani da wannan karin magana a yayin da aka saka wani abu a wajen da ake gani ya dace, sai kuma bai dace ba.)
54. Kwana nawane, maye ya yi amarya.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da ake zumudin karasowar wani abu.)
55. Ina abin yake, maye ya ci jariri.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da ake nanata wani abu da bai kara daɗa nanata shi ba.)
56. Duk a banza, talaka ya girmi sarki
(ana amfani da wannan karin mağanane a lokacin da akayi wani abu da bai yıl tasiriba)
57. Ba kukana ba, uwar köşhiya ta mutu ranar sallah.
(ana amfani da wannan karin mağanane a lokacin da aka fadava mutum wani abu da yakç ganin baruvansa)
58. Allah dai ya isa, wai anyjwa mai takaba cikl.
(ana amfani da wannan karin mağanane a lokacin da aka yıwa mutum abinda babu yadda zaiyi)
59. Kai dai ayi sha'ani, wai an cuci na kauye.
(ana amfani da wannan karin mağanane a lokacin da aka danrewa mutum wani hakkinasa)
60. Allah wadaran naka ya lalace, Rakumin dawa yaga na gida.
(ana amfani da wannan karin mağanane a lokacin da wani da aka sanshi sossai ya alkata wani abin kunya ko wani abindî bai kamataba)

Post a Comment