Hikimomi da Karin Maganganu tare da Ma'anoninsu a harshen Hausa
Kashi Na Biyu (Part 2)
Maraba da zuwa wannan shafin namu mai albarka
Gabatarwa
Daga tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al'ummar Hausawa.
Bayanin: Wannan shi ne kashi na biyu na jerin karim maganganun Hausa. Idan kuna son kashi na daya, zaku iya duba shi a shafinmu na baya.
Karin Maganganu - Kashi Na Biyu
61. Ban taba jiba, wai ance da barawo maraba.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da akakawowa mutum wani labari da bai taba jin irinsa)
62. Abin yayi yawa, shege da hauka.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da abubuwan damuwa suka taru suka yiwa mutum yawa)
63. Yaya muke ciki, wai matsiyaci yaje wajen budurwa.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da mutum yake neman mafita akan wani al'amari)
64. Abin ba dadi, wai mahaukaci yaci kashi.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da wani abu mana dadi ya faru)
65. Allah mainaita mana, wawa yaci tuwo gidan mutuwa.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da wani abin farin ciki ya samu ana taya murna)
71. Bari in tashi, wai civo yaji dare.
(ana amfarine da wannan karin maganar a yayin da mutum yayi nufin tashi daga wani waje dayake zaune)
72. Jiya ba yauba, wai toho yaga tantakwashi.
(ana amfani da wannan karin maganare a lokacin da mutum yaga wani abu sai ya tuna da wani abu da ya riga ya wuce)
73. Ni tani, Ungulu ta ga kashin dillali.
(ana fadin wannan karin magana ne a lokacin da aka umarci mutum ya aikata wani da abu yake ganin da bazai yaba)
74. Shagulatin bangalo, Ungulu taga mushen mota.
(ana amfani da wannan karin maganare a lokacin da aka fadawa mutum wata magana da bashi da alaka da ita."
75. Yau da gobe maganin mai kokari.
(ana amfani da wannan karin maganare a lokacin da mutum ya tsinci kansa a wani hali da bai taba tsammamin kasancewaa cikinsaba)
76. Wanda ya gani shi yaji kunya, wai kallon fiksarin makaho.
(ana amfani da wannan karin maganane a yayin da mutum ya aikata wani abu dashi bai damu daya aikataba amma wasu sun damu)
77. Abu yayi daidai, wai an kama ango da uwar amarya.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da komai ya daidaita ga mutum)
78. Da zaman banza, gara aikin kishiya.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da mutum yayi nufin aikata wani abu da bai zama dole ya aikataba)
79. Da kyau, wai kare yaga rawar kura.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da aka aikata wani abu daya burge mutum)
80. Tab, aiki sai da kayan aiki, zakara ya leka wandon jaki.
(ana fadin wannan karin maganane a lokacin da mutum yaga ana aiki da wasu kayan aiki da suka kamata ayi aiki dasu)
81. Salula kenan, shawara da uwar kishiya.
(ana fadin wannan karin maganane a lokacin da aka tafka wani babban shirme)
82. Abu yayi daidai, jarababbiya ta fadi a kan tsinke.
(ana fadin wannan karin maganane a lokacin da wani abu ya faru da yayiwa kowa dadi.)
83. Ta faru ta kare, an yiwa mai zani daya sata.
(ana fadin wannan karin maganane idan aka aikatawa mutum wani abu dayake ganin bashi da mafita akan abun.)
84. Na san za'a rina, wai an saci zanim mahaukaciya.
(ana fadin wannan karin maganane a lokacin da wani abu ya faru da mutum yake da yakinin dama zai faru)
85. Ban sa akaba, inji barawon hula.
(ana fadin wannan karin maganane a lokacin da ake tunanin wani ya aikata wani abu da shi kuma bai aikataba.)
86. Dama-dama, kibiya a ido.
(akan fadi wannan karin maganane a lokacin da ake ganin saukin wani abu akan wani abu)
87. Abu mai sauki, cire wando ta ka.
(ana fadin hakane a yayin da mutum yaga zai iya aikata wani abu bada bata lokaciba)
88. Bonom kenan, rufe kofa da baravo.
(ana fadin wannan karin maganane a lokacin da aka kwaba wani shirme)
89. Ina sane, wai karuwa ta taka matar aure.
(ana fadin wannan karin maganane a lokacin da mutum ya aikata abu yana sane)
90. Rashin kunya gwatso a gidan mutuwa.
(ana fadin wannan karin maganane a lokacin da wani yake aikata wata rashin kunya)
91. Wannan daban, maiam yaci kudin kida.
(ana fadin wannan karin maganane a lokacin da akc vata magana sai aka jefo vata da ba akanta akc tattauuawaba)
92. Haram, giya a gidan liman.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da aka fadawa mutum vata magana da bai yarda da itaba)
93. Dokin mazallako, Da daga ciki rokon uba kwabo.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da mutum ya cika nuna zumudi akan wani abu)
94. Aikin banza kiba a kunne.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da aka yi wani shirme a gaban mutum.)
95. Ba kukana ba, uwar kishiya ta mutu ranar sallah.
(mutum yakan fadi hakane a lokacin da aka sanar dashi wani abu da akc tumarin zai iya yin wani abu a kai kuma kai tsaye sai ya nuna bazai iyaba)
96. Sai wani jikon, kare ya zubar da tsamiyar kura.
(ana fadin wannan karin maganane a lokacin da mutum yake nufin barin wani waje da zaidauki lokaci karin ya davo wannan waje)
97. Masu abu da abinsu, wai kura da kallabin kitse.
(ana amfani da wannan karin maganane a yayin da aka ga wani da yake da wani abu kuma yama abinda yaso da wannan abu nashi)
98. Maraba gasasshe, wai kura ta ga bakin jaki.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da mutum yake kan ganiyar neman abu saikawai ya samu abin a banza.)
99. Yi yafi rashin yi, wai kazama tayitsarki da ruwan danwake.
(ana amfani da wannan karin maganane alokacin da mutum yake yin wani da baizama dole yayiba)
100. Ikon Allah, wai na kwance ya fadi.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da wani ain manraki ya faru)
101. Babu dele, zama da kaka mafadactya.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da akc kokarin tilastawa mutum aikata wani abu da bai zama dele ba a gareshi)
102. Ayi dai mu gani, in tusa zata hura wuta.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da wani yake yunkurin aikata wani da akc da tabbacin ba zai yuwuba)
103. Da wannan don wannan, wai an tura toohon banza biko.
(ana amfani da wannan karin maganane a lokacin da akc cikin wata matsala, sai kuma aka hango wata matsala daban akan wacce akc ciki)
104. Matsala dai ta auku, uban ango yayiwa amarya ciki.
(ana amfani da wannan karin magana ne a lokacin da wata matsala da babu wata mafita akanta ta auku)
105. Na rasa wajen zama, wai maquimaci ya shiga kasuwa.
(ana amfani da wannan karin maganane yayin da mutum ya rasa inda zai zama a wani waje)
106. Ana tsoron ni da iya, hiji 'yar mayya.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da mutum yake tunanin ana tsoron aikata masa wani abu.)
107. Tsautsayin takaba, aure da mai kararren kwana.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da wani abu na tsautsayi ya faru.)
108. Kudina nake ci, wai ba'audine ya ci sabulu.
(Ana fadin haka ne a lokacin da mutum yake cin wani abu da wani yake ganin shi ba zai iya ciba.)
109. Ba haka rai ya so ba, kanin miji ya fi miji kyau.
(Ana fadin haka ne a lokacin da mutum ya so samun wani abu, sai bai samu wanda bai kai shi ba.)
110. Allah Sarkin sarki, haji matar sarki ya karaya.
(Ana fadin wannan karin magana a lokacin da mutum ya ga wani abu da ya bashi tausayi, kuma bashi da halin taimako.)
111. Wannan kuma ai aikinane, wai ance da karuwa ta hau gado.
(Ana amfani da wannan karin magana ne a lokacin da aka umurci mutum ya yi wani abu da ya saba yi.)
112. Wannan kuma daban, malam ya ci kudin kida.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da ake wata magana, sai wani ya sako da wata magana da ba ita ake yi ba.)
113. Abin tuna baya, wai gyartai ya tsinci sarauta.
(Ana fadin haka ne a yayin da ake magana, sai mutum ya tuna da wani labari na damuwa da ya taba shiga a can baya.)
114. Ra'ayi kenan, kwanciya kan katanga.
(Ana fadin haka ne a yayin da mutum ya aikata wani abu wanda wani yake ganin ba zai iya yin wannan abu ba.)
115. Huta roro, waken gizo ya ki 'ya'ya.
(Ana fadin wannan karin magana ne a lokacin da mutum yake nufin yin wani abu da baya so ya yi, sai kuma ya tabbata ba zai yi ba.)
116. Karya kasa, wai boka ya binciko ranar mutuwarsa.
(Ana amfani da wannan karin magana a lokacin da aka fadi wani abu da mutum yake ganin ba zai yiwu ba.)
117. Karya ta kare, bori ya kar boka.
(Ana fadin wannan karin magana a lokacin da wani abu ya kurewa a mutum ta yadda babu wata dabara da za a bi don a aikata abin da ake so ya faru.)
118. Ba sai muga ta fadi ba, wai kwarkwata ta kayar da kyankyaso.
(Ana fadin wannan karin magana a lokacin da aka samu nasara akan wani mai yawan ji da kai ko nuna isa.)
119. Wata sabuwa, ance da shege ina ubanka.
(Ana fadin wannan karin magana a lokacin da aka zo wa mutum wata magana ko wani abu da bai san da wannan abu ba.)
120. Ni a suwa, wai cinnaka a trela.
(Ana fadin wannan karin magana a lokacin da aka saka mutum a wani abu da yake ganin ya fi karfinsa, wato ba zai iya ba.)