ISTIKHARA
GABATARWA
DAGA WANI BAWAN ALLAH
Istikhara a takaice shine: ba wa Allah zaɓi akan al'amuran ka. Neman alkhairin Ubangiji yana daga cikin abubuwan da ke sanya albarka a rayuwa. Istikhara (Neman zabin Allah) na da matuƙar muhimmanci a cikin lamura.
Jabir Bin Abdullahi Allah Ta'ala ya riƙa faɗa, cewa Manzon Allah (S.A.W) yana koya mana yadda ake yin istikhara a cikin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga cikin Alqur'ani.
ADDU'AR ISTIKHARA
اللّٰهُمَّ إِنِّيْ أَسْتَخِيْرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأَسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ العَظِيْمِ فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلاَ أَقْدِرُ، وَتَعْلَمُ وَلاَ أَعْلَمُ، وَأَنْتَ عَلاَّمُ الغُيُوْبِ اللّٰهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأمْرَ (وَيُسَمِّيْ حَاجَتَهُ) خَيْرٌ لِيْ فِيْ دِيْنِيْ وَمَعَاشِيْ وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاقْدُرْهُ لِيْ وَيَسِّرْهُ لِيْ ثُمَّ بَارِكْ لِيْ فِيْهِ وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الْأَمْرَ شَرٌّ لِيْ فِيْ دِيْنِيْ وَمَعَاشِيْ وَعَاقِبَةِ أَمْرِيْ فَاصْرِفْهُ عَنِّيْ وَاصْرِفْنِيْ عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ، ثُمَّ أَرْضِنِيْ بِهِ.
FASSARA:
Ya Allah, ina neman zabinka domin ilminka, kuma ina neman ka bani iko domin ikon ka, kuma ina rokonka daga falalarka mai girma. Kai ne mai iko, ni kuwa bani da iko, kuma Kai ne masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan da ba a gani. Ya Allah! Idan kasan cewa wannan al'amari (sai ka ambaci bukatar ka) alheri ne a gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen al'amarina, to ka qaddara mini shi, kuma ka saukake mini shi. Sannan ka albarkace ni a cikin sa; idan kuma kasan cewa wannan al'amari sharrine a gare ni a cikin addinina, da rayuwata da karshen al'amarina, to ka kawar da shi daga gare ni, kuma ka kawar dani daga gare shi. Ka kaddara mini alherin a duk inda yake, sannan ka sanya ni in yar da shi.
TSOKACI: RAKA'O'INTA:
Ana yinsa da raka'a 2, wasu malaman suna ganin zaka iya yin sama da raka'a biyu.
DA WANE LOKACI YA KAMATA KA YI TA?
Ana iya yin istikhara a kowani lokaci, amma mafi alkhairi a cikin dare. Banda lokacin da aka hana yin nafila.
A INA AKE ADDU'AR?
Wasu malaman sun ce ana yi lokacin sujuda, wasu sun ce a zaman tahiya bayan an gama yi wa Annabi (S.A.W) salati kafin a yi sallama, wasu sun ce ana yi bayan sallama. Wasu masana sun ce yana da kyau a fara yin istikhara sannan a nemi shawara daga mutum mai kyau.
WANI ZAI IYA YIMA WANI?
Wasu masana sun ce wanda ba zai iya yin istikhara ba, to zai iya yi masa. Ana yin istikhara ga abubuwan da suka shafi al'amura kamar aure, aiki, tafiya, karatu, kasuwanci da sauran abubuwan rayuwa. Kowa na da hakkin yin istikhara.