Allah ya daukaka wadan nan kwanaki da falala mai tarin yawa wadanda bai sanya su ba a wani watan da ba shi ba.
[FALALAR KWANAKI GOMA NA ZUL-HIJJAH]
-
Sune kwanaki sanannu a wajan Allah wadanda ake aiyukan ibada mafi girma acikin kwanakin shekara baki daya. Allah yana cewa:
{ وَيَذْكُرُوا اسْمَ اللَّهِ فِي أَيَّامٍ مَعْلُومَاتٍ عَلَى مَا رَزَقَهُمْ مِنْ بَهِيمَةِ الْأَنْعَامِ }
-
Allah yayi Rantsuwa da wadannan kwanaki acikin suratul Fajr.
{ وَالْفَجْرِ (1) وَلَيَالٍ عَشْرٍ (2) }
-
Cikin goman farko ake kabarbari sabanin sauran watanni.
اللّهُ أَكْبَرُ، اللّهُ أَكْبَرُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، اللّهُ أَكْبَرُ، اللّهُ أَكْبَرُ، وَلِلَّهِ الْحَمْدُ
مَا مِنْ أَيَّامٍ أَعْظَمُ عِندَ اللَّهِ وَلَا أَحَبُّ إِلَيْهِ مِنَ الْعَمَلِ فِيهِنَّ مِنَ الْعَشْرِ، فَأَكْثِرُوا فِيهِنَّ مِنَ التَّهْلِيلِ وَالتَّكْبِيرِ وَالتَّحْمِيدِ.
-
Acikin kwanakin ne ake yin Azumin ranar Arfa ga wanda baije aikin Hajji ba, wanda Azumi yana kankare zunuban shekara guda biyu.
Manzon Allah s.a.w yana cewa; *(Yin Azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekara mai zuwa)*
- Watan Zul Hijjah shine cikamakin watanni sanannu wanda Allah yace { الْحَجُّ أَشْهُرٌ مَّا عْلُومَاتٌ }.
-
Mafi sune mafi Alkhairi da falalar kwanakin duniya baki daya.
مَفِي الْخَيْرِ يَوْمٍ أَعْظُمُ الْكَثَابِرِ فِي الْعَشَرَةِ الْأُوَلِ مِنْ ذُو الْحجة.
-
Ibn Hajar RH.A ya ce: Acikin Fathul Barry dalilin da yasa wadannan kwanakin sukafi albarka fiyeda sauran kwanaki shine;
Allah ya shar'anta ibada mafiya tsada acikinsu kamar su; Sallah da azumin da Sadaka da aikin hajji da sauran ibadun na musamman wadanda ba'ayinsu sai awadannan kwanakin kadai.
-
Hadisi ya tabbata cikin Bukhari daga dan Abbas R.A Yace: Annabi S.A.W yace:
مَا مِنْ أَيَّامٍ الْعَمَلُ الصَّالِحُ فِيهَا أَفْضَلُ مِنْ هَذِهِ الأَيَّامِ الْعَشْرِ، قَالُوا وَلَا الْجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ؟ قَالَ وَلَا الْجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ إِلَّا رَجُلٌ يَخَاطِرُ بِنَفْسِهِ وَمَالِهِ وَلَمْ يَرْجِعْ مِنْ ذَلِكَ بِشَيْءٍ.
- A cikin wadannan kwanakinne ake yin ayyukan Hajji da Umara da sauran ibadu mafiya tsada.
- Acikin wadannan kwanakine akiyi layya da idin babbar sallah kuma suna cikin mafiya tsarar ayyuka da akeyi acikin wadannan kwanaki wadanda ba'ayi acikin wadansunsu.
Allah ka sadam da alkhairi wadannan ranaku kuma ka abamu ikon yin ayyukan alkhairi acikinsu. Amin.