JAMB Ta Sake Bayyana Sabon Mafi Ƙarancin Maki Na Shiga Manyan Makarantu a Shekarar 2025/2026
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandare ta Ƙasa (JAMB) ta bayyana sabon tsarin mafi ƙarancin makin da ɗalibai za su samu domin samun gurbin karatu a jami’o’i, kwalejojin ilimi, da makarantun fasaha a kakar karatu ta 2025/2026.
Sabbin makin sun fito ne a lokacin babban taron shekara-shekara na tsara manufofin karɓar ɗalibai (Policy Meeting), wanda aka gudanar a cibiyar taro ta Bola Ahmed Tinubu dake Abuja. Taron ya samu halartar shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, da wakilan jami’o’i, kwalejojin kimiyya, polytechnics, da sauran hukumomin ilimi daga faɗin ƙasar.
Sabon Tsarin Mafi Ƙarancin Maki Da Aka Amince Da Su:
150 – Domin shiga jami’o’i
140 – Domin shiga kwalejojin kimiyyar jinya (nursing)
100 – Domin shiga kwalejojin ilimi da na fasaha (polytechnics)
Farfesa Oloyede ya bayyana cewa wadannan su ne mafi ƙananan makin da ɗalibai za su iya samu domin su samu damar shiga tsarin CAPS – tsarin dijital da JAMB ke amfani da shi wajen tantancewa da karɓar ɗalibai.
Ya kara da cewa kowace makaranta na da ‘yancin ƙara matsayin makin shiga bisa fannin da ɗalibin ke nema, matuƙar ba ta sauka ƙasa da ƙayyadadden makin da aka amince da shi ba.