Wacece Maryam Malika Wacce Zata Auri Abdul M Sharif ?
Maryam Mohammed, wacce akafi sani da Maryam Malika, ta kasance Daya daga Cikin jaruman Masana'antar 𝗞𝗮𝗻𝗻𝘆𝘄𝗼𝗼𝗱 mafi kaurin suna a shekarar 2010/2012, Tayi tashe sosai a lokacin tare da samun damar fitowa a Manyan Fina-finai a lokacin tare da manyan jarumai.
Tun kafin jarumar ta Fara fitowa a film a matsayin cikakkiyar jaruma an taba nuna jarumar a cikin wani film tare da Yayarta Margayiya Balaraba a lokacin batafi shekara shida ba a duniya.
Ta fara fitowa a cikin film dinta na farko Mai suna WASILA(2010) kafin daga baya muka ganta a film din SOYAYYAR FACEBOOK, Wanda Mutane suka dauka shine film dinta na farko a lokacin, Malika ta ida sanuwa a duniya ne bayan fitar Shirin 𝙈𝘼𝙇𝙄𝙆𝘼,𝙆𝙊𝙉𝘼 𝙂𝘼𝙍𝙄, 𝘼𝘿𝙊𝙉 𝙂𝘼𝙍𝙄, 24 𝙃𝙊𝙐𝙍𝙎, 𝙉𝘼 𝙂𝘼𝙉𝙄 𝙄𝙉𝘼𝙎𝙊, 𝙅𝘼𝙍𝙄 𝙃𝙐𝙅𝙅𝘼, 𝙆𝙐𝙉𝙔𝙄 𝙎𝘼𝙆𝙀, 𝙎𝘼𝙇𝙈𝘼, Dadai Sauransu.
Bayan jarumar tayi Aure na dan wani lokacin ta sake dawowa Masana'antar 𝗞𝗮𝗻𝗻𝘆𝘄𝗼𝗼𝗱 bayan Shekara Goma, a cikin Shirin DA ACE BABU ZUCIYA, IZZAR SO, GARGADA, KE DUNIYA, MANYAN MATA,DAN JARIDA da Kuma KISHIYATA Wanda kusan shine Wanda yafi Nasara a cikin fina-finai jarumar kasancewar itace take jagorantar Shirin.
Maryam Malika itace jaruma ta uku bayan Fati Mohammed, Zara Diamond, wayan da bayan aurensu ya Mutu Sukan dawo kannywood Kuma suka sake karbuwa a gurin Yan kallo sabanin Sauran jaruman da suke gagara karbuwa idan suka Dawo.
Duk da dai ita jaruma sadiya kabala ta rungumi kasuwanci bayan mutuwar aurenta.
A ranar jumaa me zuwa 27 ga watan yunin nan da muke ciki na 2025 za’a daura auren jaruma malika da Abdul m Shareef yaya ga Fitaccen mawakin nan Umar m Shareef a jihar kaduna.
Wanne fata kuke dashi gareta da Angonta Abdul?