Sabuwar Jarumar Kannywood Daga Sokoto Birnin Shehu
Wannan ita ce jaruma mai suna Zainab Muhammed wadda aka fi sani da Zainab Diyana, wacce ta kasance matashiya ce mai tashe a jihar Sokoto a fagen wasannin hausa musamman a sha'anin fina finai da wakoki.
[Hoton Zainab Diyana a wani fim]
Ilimi da Addini
- Ta yi karatun nursing
- Ta yi saukar Alqur'ani mai girma a matakin addini
Ayyukan Kasuwanci
Tana da kamfanin siya da siyar da kayan makulashe mai suna 'Deeyana collection and confectionery'. Matashiya ce mai fafutukar neman na kanta a fagen kasuwanci.
Aikin Fina-Finai da Waƙoƙi
[Hoton Zainab Diyana a fim din 'Ali Baba']
- Tana shahara a duk fadin jihar Sokoto da kewaye
- Ta taka rawar gani a fina-finan hausa kamar "Ali Baba"
- Ta sami lambobin karramawa daban-daban
- Ta lashe lambar yabo ta "Best Actress"
Burin Rayuwa
"Ni a yanzu ba abunda nafi so bayan na ganni a gidan miji shine babban burina. Ina neman addu'ar al'umma da su taya ni da addu'ar Allah ya bani miji na gari."
Ci Gaba da Aiki
Jarumar tana cigaba da taka rawar gani a sha'anin harkokin wasannin fina finai da wakokin Hausa, a yayinda yanzu hakan tana cigaba da aiki tare da:
- Manyan daraktoci
- Furodusoshi
- Mawaka daga wurare daban-daban
Zainab Diyana ta kasance misali ga matasa mata masu burin samun nasara a fagen fina-finai da kasuwanci. Wanne fata za ku yi mata?
Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto