Takaitattun Labaran Yau
Shugaba Tinubu ya mayar da martani kan zargin jam'iyya É—aya
Shugaba Bola Tinubu ya mayar da martani game da zargin da ƴan adawa ke wa jam'iyya mai mulki na cewa tana son mayar da ƙasar kan tsarin jam'iyya ɗaya.
Zanga-zangar ranar dimokuraÉ—iyya
Masu zanga-zanga sun fito a biranen Najeriya domin kokawa kan halin da ƙasar ke ciki yayin da ƙasar ke bikin ranar dimkuraɗiyya a yau Alhamis.
Sojoji sun kashe Auta da wasu 13 a Zamfara
Sojoji sun kashe Auta, Ƙasurgumin dan ta'adda da wasu 13 a Yammacin karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Zulum ya yi afuwa ga fursunoni 66
Ranar DimokuraÉ—iyya: Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri.
Sanata Ndume ya yi kira kan tallafin hajji
Sanata Ali Ndume yace ya kamata a dawo da tallafin aikin hajji ga maniyyatan Najeriya.
An hana hawa babur da daddare a Gombe
An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe.
Guguwa ta kashe mutane shida a Taraba
Wata mummunar guguwa ta yi sanadin mutuwar mutum shida sannan ta jikkata wasu 30 a garin Garba-Chede da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba.
Harin kauyen Nkiendowro ya kashe huÉ—u
Aƙalla mutum huɗu ciki har da jaririn wata tara aka kashe a wani hari da aka kai ƙauyen Nkiendowro da ke Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato.
Rashin wutar lantarki ya yi wa Arewa maso Gabas illa
Rashin wutar lantarki a Arewa maso Gabas ya janyo wa jama'a da 'yan kasuwa asarar dukiya, sakamakon aikin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN), ke yi na aikin sabbin turakun wutar lantarki.
Yunkurin kashe kansa a Gusau
Wani ma'aikacin gidan gyaran hali yayi yunkurin kashe kansa a Gusau babban jihar Zamfara.
Jirgin Air India ya yi hatsari
Jirgin saman kamfanin sufurin Air India É—auke da fasinjoji 242 ya yi hatsari jim kaÉ—an bayan tashi a birnin Ahmedabad da ke yammacin Indiya.
Nijar ta rage ma'aikatan jakadancinta
Nijar ta rage adadin ma'aikatan da ke aiki a ofisoshin jakadancinta.
Ƙungiyar likitoci ta Indiya ta ba da rahoton gaggawa
Ƙungiyar likitoci ta ƙasar Indiya ta ce an garzaya da ɗalibai masu karatun likitanci 50-60 zuwa asibiti bayan da jirgin Air India da ya yi hatsari ya faɗa kan gidan kwanan ɗaliban.
Amurka za ta fice daga Iraƙi
Amurka za ta kwashe ma'aikatanta daga Iraƙi kan rikicin Isra'ila da Iran.
An zako gawarwaki 200+ daga jirgin Indiya
An zaƙulo gawarwaki sama da 200 daga jirgin Indiya da ya yi hatsari.
Rikicin siyasa ya kashe mutane uku a Bolivia
An kashe akalla mutum 3 a tsakiyar ƙasar Bolivia sakamakon mummunar arangama ta siyasa.