Yanzu: Babban Layin Wutar Lantarkin Najeriya, ya sake faɗuwa karo na 11 a shekarar 2024.


Yanzu: Babban Layin Wutar Lantarkin Najeriya, ya sake faɗuwa karo na 11 a shekarar 2024.

Wannna na cikin wata sanarwa da Hukumar Gudanar da Tsarin Wutar Lantarki ta Ƙasa (ISO), reshen Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), ta fitar. 

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ofishin dake kula da babban layin wutar lantarki a Najeriya, ya ce layin ya sake daukewa da misalin karfe 2 da minti tara na rana agogon kasar a ranar Laraba. Cikin sakon, ofishin ya ce tuni aka fara kokarin dawo da layin bakin aiki. Daukewar babban layin wutar lantarkin da ake yawan samu a kasar, na janyo babbar asara musamman ga 'yan kasuwa wadanda ke neman kudi ta hanyar amfani da lantarki. 

Ofishin, ya nemi afuwar al'ummar Najeriya, yana mai cewa tuni aka dukufa don dawo da wutar. An samu daukewar babban layin wutar lantarkin sau 12 ke nan tun daga farkon shekarar 2024 kawo yanzu. Babban layin wutar lantarki na Najeriya - power grid a Turance - gungun layuka ne da suka haɗa tashoshin samar da lantarki da ke bai wa dukkan sassan Najeriya wuta. A taƙaice, wata ma'dana ce da ke ɗauke da dukkan lantarkin da ake sha a Najeriya.

 Haka nan, ba wani wuri ba ne guda ɗaya, tarin layuka ne a wurare daban-daban. An tsara shi ne don ya yi aiki ta wasu taƙaitattun hanyoyi musamman dangane da yawan wutar da ake da ita, da tsaron lafiyarsa.

Post a Comment

0 Comments