GA WATA DAMAR GA MASU BUKATA
Litinin, 28 ga Yuli, 2025 ne National Directorate of Employment (NDE) ta buɗe portal ɗin rajista domin fara 2nd Phase na shirin Renewed Hope Employment Initiative (RHEI) 2025.
Za a rufe portal ɗin rajista a ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025. Wannan dama ce ta musamman ga matasa masu shekaru daga 18 zuwa 45 da sauran masu neman aikin yi a Najeriya.
Abubuwan da ya kamata ku sani daga Phase na 1:
- Yawancin wadanda suka shiga sun sami tallafi da kayan aiki da lamunin kasuwanci.
- Wasu sun samu rance daga N10,000 zuwa N500,000.
- Wasu sun karɓi kayan aiki kamar kwamfuta, laptop, kayan aikin gyaran aski, saloon, keken dinki, da sauransu.
- An bada tallafin kudi kai tsaye kamar N60,000, N30,000, N20,000, da N10,000.
- Fiye da kashi 87% sun riga sun karɓi tallafi, wasu suna jiran biyan su kafin ko bayan an bude sabon portal.
Menene Renewed Hope Employment Initiative (RHEI)?
Shirin RHEI na gwamnati ne wanda ke baiwa matasa horo kyauta a fannoni daban-daban na sana'o’in hannu, noma, kasuwanci, da fasahar zamani, tare da tallafi na kuɗi da kayan aiki don fara ko habaka sana'o'i.
Abubuwan Amfani da Phase na 2
- Horo: Sana’o’in hannu kamar dinki, gyaran aski, gini, wutar lantarki, da sauransu.
- Agriculture: Horo da tallafin kayan gona da dabarun noma.
- Kasuwanci: Hanyar gudanarwa da bunkasa kananan kasuwanci, da tallan yanar gizo (digital marketing).
- Tallafi: Biya na kudi daga N10,000 har zuwa N500,000 ko kayan aiki masu amfani.
- Takardar Shaida: Masu horo za su sami takardar shaidar kammala horo.
- Lamuni: Damar samun rancen kudi da ƙaramin ruwa domin fara ko fadada kasuwanci.
Yadda Za Ka Yi Rijista
- Ziyarci adireshin yanar gizon rasmi na NDE: https://nderegistrationportal.ng/
- Cika cikakkun bayananka ciki har da NIN da hoton fasfo na baya-bayan nan.
- A tabbatar an cika dukkan bayanai tare da duba su kafin aika su.
- Jira sakamakon tantancewa daga hukumar NDE.
Ka hanzarta yin rajista kafin lokaci Ya Kure. Wannan dama ce ta canza rayuwarka ta hanyar samun horo, tallafi, da damar kafa sana’a ko aiki mai kyau.
0 تعليقات