Aisha Buhari Ta Nemi 'Yan Najeriya Su Yafewa Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari Kafin A Kai Shi Kabari.
Abuja, Najeriya – Aisha Buhari, matar tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa mijinta ya bar mata wasiyya ta musamman kafin rasuwarsa, inda ya roƙa gafarar 'yan Najeriya kan kura-kuren da ya aikata a lokacin mulkinsa.
A cewar Aisha, tun bayan saukarsa daga mulki a 2023, Buhari ya saba gaya mata cewa idan Allah ya karɓi rayuwarsa kafin ita, to ta isar da sakonsa ga 'yan Najeriya domin su yafe masa.
"Tunda ya sauka daga mulki, maganar da yake yawan faɗa min a duk lokacin da muke hira ita ce, idan ya riga ni mutuwa, in isar da saƙon sa ga ƴan Najeriya cewa su yafe masa kura-kuren da ya yi a mulkinsa, kasancewar sa ɗan adam mai yin dai-dai da rashin dai-dai," Aisha ta bayyana da hawaye.
Ta ƙara da cewa: "Don haka, don Allah ina roƙon kowa da kowa ya yafe masa tun kafin a kai shi makwancinsa."
Aisha ta bukaci al’umma su yada wannan saƙo domin kowa ya sani, tana mai fatan Allah ya gafarta masa kurakuran rayuwarsa kuma ya jikan sa da rahama.
Marigayi Buhari ya rasu a London bayan doguwar jinya, kuma za a dawo da gawarsa gida domin binne shi bisa tsarin Musulunci.
إرسال تعليق