FGN TVET Initiative: Za a Fara Bayyana "APPROVED" a Dashboards Nan da Sati Biyu
A cikin wata hira ta musamman da aka yi da ita a tashar NTA (Nigerian Television Authority) cikin safiyar yau, Dr. Nabila Mohammed, wadda ke rike da matsayin mataimakiya ta musamman ga Ministan Ilimi kan harkokin TVET da STEMM, ta bayyana cewa cikin sati daya zuwa biyu (1–2 weeks) za a fara ganin matsayi na "APPROVED" a dashboard na waɗanda zasu ci gajiyar shirin TVET na Gwamnatin Tarayya.
Mahimman Bayanai:
- Za a fara ganin matsayi na "APPROVED" a dashboard nan da sati 1-2
- Duk shirye-shiryen NBTE sun kammala
- Ana gudanar da tantancewa da kammala jerin masu cancanta
- Bayanin zai bayyana a shafin dashboard na shirin TVET
A cewar Dr. Nabila, duk shirye-shirye sun kammala daga bangaren NBTE (National Board for Technical Education), kuma yanzu ana aikin tantancewa da kammala jerin jadda walin waɗanda suka cancanci ci gaza zuwa mataki na gaba.
Wannan sanarwa na nufin cewa masu neman shirin TVET (Technical and Vocational Education and Training) na Gwamnatin Tarayya za su iya sa ran ganin matsayinsu na amincewa a cikin dashboard din shirin nan ba da dadewa ba.
Ana sa ran wannan mataki zai ba wa jama'a cikakken bayani game da matsayin aikace-aikacensu, wanda zai sauƙaƙa tsarin shiga cikin wannan muhimmin shiri na ilimi da horarwa.
Yadda Za a Duba Matsayi a Dashboard
Masu neman shirin za su iya:
- Shiga shafin dashboard na shirin TVET
- Shiga cikin asusunsu ta amfani da login details
- Duba sashin "Application Status"
- Za a ga alamar "APPROVED" idan an amince da su
Ana kuma sa ran za a aika sanarwa ta imel da SMS ga waɗanda aka amince da su don sanar da su game da ci gaba zuwa mataki na gaba na shirin.