Stay connected with us Apkstore for Get Latest Update Now. apkstore.com.ng

Takaitattun Labaran Duniya Na yau

Safiyar Lahadi 15/06/2025CE - 19/12/1446AH

Safiyar Lahadi 15/06/2025CE - 19/12/1446AH

Ga Takaitattun Labaran

Harin 'Yan Bindiga a Benue

An fargabar cewa an kashe akalla mutum 100 a wani hari da 'yanbindiga suka kai garin Yelewata da ke yankin karamar hukumar Guma da ke jihar Benue.

Kisan Ma'aikacin Jami'a a Kano

Masu kwacen waya sun kashe wani ma'aikacin Jami'ar Northwest da ke Kano, Buhari Imam, ta hanyar daba masa wuta.

Sulhu a Katsina

Al'ummar Katsina sun yi sulhu da Ado Aleru da wasu manyan yanfashin daji.

Tattaunawar Siyasa a Kano

Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya gudanar da wani zama da 'yan soshiyal midiyarsa da zummar ƙarfafa manufofinsa na siyasa.

Rikicin Iran da Isra'ila

Kasar Iran ta ci gaba da yin ruwan makamai masu linzami a daren Lahadi kan Isra'ila, yayin da ita ma Isra'ilar ta ce ta tana ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin soji a Tehran. Hare-haren sun kashe mutum 12 tare da jikkata sama da 130.

Farautar Dan Bindiga a Amurka

'Yansanda a jihar Minnesota ta Amurka na ci gaba da farautar wani danbindiga da ya harbe wata 'yar majalisar dokokin jihar tare da mijinta, ya kuma raunata wasu mutum biyu.

Shugabannin Rasha da Amurka Sun Tattauna

Shugaban Rasha da na Amurka sun tattauna a kan rikicin Isra'ila da Iran.

Download free APK files and Android apps from APK Store. Explore safe, verified, and updated Android applications across multiple categories...

إرسال تعليق