DOLLAR COST AVERAGE (DCA):
DCA wani salo ne da me shiga kasuwa (Investor) yake bi wajan shiga kasuwa.
Yadda salon yake shine: yana rarraba kuɗin shiga kasuwar zuwa gida gida.
kamar Misali ya ware $1k domin shiga kasuwa, To sai ya rarraba ta zuwa gida 5, sai ya kasan ce duk bayan sati ɗaya zai dinga zuba $200 har zuwa 5weeks. Wannan salon shiga kasuwar shine ake kira da DOLLER COST AVERAGE (DCA).
Bari na ƙara muku wani misali domin fahimtar tsarin sosai:
Let's say:
Ka shirya zaka yi investing $100 a $SOL.
To a Normal investment zaka ɗauke ta ne ka siya shi a lokaci ɗaya.
Amman idan har DCA Approach zaka yi Sai ka zuba $50 yau, Next week Ka zuba ragowar $50..
Ko kuma ka rabata gida 5:
Duk sati ka zuba $10 zuwa sati 10weeks, ka kammala zuba wannan doller $100.
To Amman, menene Advantage ɗin yin shi wannan Doller cost average ɗin?
- Sannan wane Alfanu yake bawa me shiga kasuwa!?
- Bari na Amsa wannan tambayer dake yawo a zuciyar ka!☺️
Kamar yadda yake a kowa ce irin kasuwa akwai masu cinikayyar zangon Lokaci (Long term investors).
- Da kuma masu cinikayyar gajeren Lokaci (Short term Investors).
Muma a kasuwar crypto muna da su!
Duka waɗannan ɓangarorin tsarin DCA na matuƙar taimaka musu a cikin kasuwa ta hanyar basu damar takaita asara a cikin kasuwa.
Misali:
Ka shirya zaka siyi Coin da $1k. idan ka zuba duka kuɗin a lokaci daya, kuma sai aka samu rashin Sa'a a rana ɗaya farashin COIN ɗin ya sauka da -10%. Hakan na nufin ka rasa $100.
Amman idan da zaka bi wannan tsarin na DOLLER COST AVERAGE, ya kasan ce ka raba wannan kuɗin naka zuwa gida 4, ma'ana $250 kenan. Sai ya zamana ka shirya zaka dinga shiga duk bayan sati ɗaya!.
To da kuwa a lokacin da wannan coin ɗin ya faɗi da -10%, zaka yi asarar $25 ne kawai.
Sannan kuma maybe lokacin da sati zai zagayo zata iya yiwuwa wannan COIN ɗin ya tashi a lokacin, kaga kenan zaka kasan ce a (Break even). Ma'ana babu riba babu Asara!
Sannan kuma opportunity ne a wajan ka, kayi Amfani da wannan damar ta faɗuwar da farashin COIN ɗin yayi a wannan lokacin ka siye shi a sauƙi da ragowar kuɗin.
Kaga kenan zai kasan ce lokacin da zai koma wannan farashin daya faɗo, kuɗin ka suna nan a $1k . Wannan shine Hikimar yin DCA!
Wannan a ɓangaren Investors kenan!
A fannin Trader ma:
Shima Trader da yake Amfani da Technical Analysis wajan shiga kasuwa yana iya raba abun da yayi niyyar shiga kasuwar dasu, ko kuma fita kasuwa dasu. Ta hanyar Amfani da: 1 TP, 2 TP, 3 TP.
TP = Take Profit.
Sai ya kasan ce Da zarar yaga kasuwa tayi Breaking wani Resistance sai ya shiga da 50% na jarin. Da zarar ta dawo yin Retest sai ya zuba sauran.
Idan kuma kasuwar bata dawo wannan Resistance ɗin ba data fasa Kaga still Yana cikin kasuwar.
DCA tsari ne ke kyau wanda yake taimakon ƴan kasuwa sosai.
Kuma tsari ne da duk wani Successful Trader/Investor yake Amfani dashi wajan shiga kasuwa
zaka iya shirya CALENDAR 📆. Wanda zata dinga tuna maka a cikin wayarka.
Wannan shine bayanin da zanyi a takaice, idan ka ƙaru kayi sharing domin wasu ma su Amfana.