Bola Tinubu: ya gabatar da kasafin kuɗi na naira tiriliyan 47.9 ga majalisun dokoki Shugaban Ya gabatar Da kasafin kuɗin ƙasar na .2025

APK Store
0

Bola Tinubu: ya gabatar da kasafin kuɗi na naira tiriliyan 47.9 ga majalisun dokoki Shugaban Ya gabatar da kasafin kuɗin ƙasar na 2025 ga majalisun dokokin ƙasar.

Kasafin dai wanda ya kai yawan naira tiriliyan 47.9, shi ne irinsa na biyu da shugaban ke yi tun kama aikinsa a shekarar 2023.

Tinubu ya bayyana kasafin kuɗin da kasafin da aka yi domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar.

Batun raya ƙasa da samar da kayan more rayuwa su ne ƙashin bayan wannan kasafin na shekarar 2025.” In ji Tinubu.

Shugaban ya yi taƙaitaccen bayani dangane da kuɗaɗen da aka ware ga ma’aikatun da ya ce zai fi bai wa muhimmanci a kasafin kamar haka:

Tsaro – naira tiriliyan 4.91Samar da kayan more rayuwa – naira tiriliyan 4.06Lafiya – naira tiriliyan 2.48 Ilimi – naira tiriliyan 3.52.

A ranar Litinin ne dai majalisar zartarwar kasar ta zartar da kasafin kuɗin na 2025.

Majalisun guda biyu wato na dattawa da wakilai dai za su yi duba na tsanaki domin yin gyara ga kasafin kafin ya zamo doka.

  • “Za mu zauna mu yi karatun ta nutsu domin tsefe kasafin inda za mu tabbatar an yi wa ɓangarori da ma’aikatu adalci. Idan akwai matsala to aikinmu ne mu gyra shi”. In ji Sale Soli Jibiya, ɗan majalisar wakilai ta ƙasar.

Ina za a samo kuɗin kasafin?

An dai ɗora kasafin kuɗin na 2025 na Najeriya ne a kan dala 75 a kan kowacce gangar ɗanyen mai guda kuma ana sa ran Najeriyar za ta samar da gangar ɗanyen man fiye da miliyan biyu a shekarar mai kamawa.

Shugaba Bola Tinubu ya shaida wa majalisun dokokin cewa muna fatan samun naira tiriliyan 34.82 ta hanyar kuɗin shiga domin zuba wa a kasafin.

Tinubu ya ce kasafin na da giɓin naira tiriliyan 13.08 wato kaso 3.08 na kasafin.

Ana dai hasashen cewa gwamnatin za ta ciyo bashin naira tiriliyan 13 daga gida da waje domin cike giɓin da kasafin ke da shi.

Kasafin mai yawan naira tiriliyan 47.96 dai ya ɗara na shekarar da ta gabata da kaso 36.8.

Abubuwan da Tinubu ya faɗa wa majalisa:

Ina farin cikin sanar da ku cewa gwamnatinmu ta yi rawar gani wajen ƙaddamar da kasafin kuɗi na 2024, inda muka cimma kaso 75 na abin da muka saka agaba a watanni taran shekarar ta hanyar samun kuɗaɗen shiga masu yawan naira tiriliyan 14.55.

Tattalin arziƙin Najeriya ya samu haɓaka da kaso 3.46 a watanni taran 2024, ƙarin a kan kaso 2.54 a watannin taran 2023.Asusun Najeriya na ƙasar waje yanzu haka ya kai kusan dala biliyan 42 wanda ya samar da kariya daga duk wata komaɗar tattalin arziƙi da ka iya tasowa.Tsaro shi ne gimshiƙin cigabanmu.

Mun sanya kuɗaɗe masu yawa a harkar sojoji da ƴansanda domin samar da tsaro a ƙasar, tsare iyakokinmu.Lokacin da muka ƙaddamar da gidauniyar raya ababan more rayuwa, muna da yaƙinin cewa ababan more rayuwa su ne ƙashin bayan cigaban tattalin arziƙi.Mun fahimci cewa al’ummarmu su ne arziƙinmu shi ya sa muke zuba kuɗaɗe a fannin ilimi da lafiya da sauran fannonin walwalar jama’a.Ba za mu taɓa juya baya ga samar da abinci ba.

Wannan ne ya sa muke tallafa wa manomanmu da kuɗaɗe da kayan noma domin dawo da ƙimar noman wanda zai bayar da tabbacin cewa babu wani ɗan Najeriya da ke fama da yunwa.Ƙasarmu na fuskantar barazanar gushewa daga matsalar rashawa da cin hanci da kuma rashin tsaro. Waɗannan matsalolin ba wai ba za a iya maganinsu ba, hakan zai yiwu amma sai idan mun haɗa ƙarfi da ƙarfe.

Tags

إرسال تعليق

0 تعليقات
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.
إرسال تعليق (0)
Our website uses cookies to enhance your experience. Learn More
Accept !